Bayar da ladan karanta Alkur’ani ga mamaci
Tambaya
Shin ya halatta a bayar da ladan karanta Alkur’ani ga mamaci?
Amsa
Abin da ya tabbata a cikin shari’a shi ne lallai karanta Alkur’ani da bayar da ladansa ga mamaci abu ne da ya halatta, ladan kuma yana isa zuwa ga mamacin ya kuma amfane shi in Allah ya yarda; saboda maganar da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi Amru Bn al- Asi (Allah ya kara yarda da shi) cewa: (Lallai in dai Musulmi ne kuka ‘yanta bawa a maimakonsa, ko kuka yi sadaka a maimakonsa, ko kuka yi aikin Hajji a maimakonsa za su isa zuwa gare shi) [Abu Dawud]. Wannan sai ya nuna cewa lallai ladan karatun Alkur’ani yana isa ga mamaci; domin babu wani bambanci tsakanin a ce ‘yanta bawa, da sadaka da aikin Hajji sun amfane shi, da kuma a ce karatun Alkur’ani ya amfane shi. lallai malaman fikihu sun bayyana cewa duk wani ayyukan neman lada da za a yi a sanya ladan ga mamaci, to kuwa zai amfane shi da ikon Allah mai girma. Ya kamata a duk sanda Musulmi zai karanta Alkur’ani ya kyautata niyyarsa wajen karatun, ya yi saboda Allah shi kaxai, ya kuma karanta cikin tsoron Allah, tare da tadabburi.