Rangwame

Egypt's Dar Al-Ifta

Rangwame

Tambaya

Mene ne ma’anar rangwame

Amsa

Lallai Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) shi ne babban abin koyi wajen rangwame, akan turbarsa ce masu koyi da koyarwarsa suka tafi a tsawon tarihi, da kuma fadin kasar Allah, wannan sifa ta bayyana a cikin halayen Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a cikin tarihnsa mai albarka, tun kafin hijira da bayan hijira, inda ya aiwatar da wannan dabi’a ta rangwame da hakuri a garin Makka, tun kafin hijira, bayan hijira kuma ta zama tsari ne na rayuwa, inda ta zama doka daga cikin dokoki, kuma ka’ida tabbatacciya, dangantaka ce ta kyautata hali, tun daga ranar da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya shiga Madina, inda ya bude garin da kira zuwa ga zaman lafiya, da taimakekeniya, da rayuwar tare, da tsarin ‘yan kasa.

Share this:

Related Fatwas