Yin salati ga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam)
Tambaya
Mene ne hukuncin yiwa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ta sigar da ba ita ce ta zo a sunnah ba?
Amsa
Yiwa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya halasta da kowani irin siga, shin ta zo a sunnah ko ba ta zo ba, kai ko da daga cikin na gwaji ne, matukar dai salatin ya dace da matsayin Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam).
Babu bukatar kallon abin da wadansu masu bidi’antar da wadannan sigogin suke bayyanawa, shi dai umurnin Allah akan yin salati da neman tsira ga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya kunshi bayyana girmansa da daukakansa, da girmama sha’aninsa, da daukakan matsayinsa, Allah Mai girma yana cewa: (Domin ku yi imani da Allah da manzonsa ku girmamashi ku darjantashi) [Alfatah:9], hakika kamar dai yanda sunnar Annabi tazo da umurni na kyautata yin salati ga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) inda yake cewa: (Ku sani cewa ana bijiromini da sunayenku da kamanninku, don haka ku kyautata yimin salati) Abdullahi bin Mas’ud (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “Idan ku kayi wa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) to ku kyautata yi masa salati” Allah Mai girma da daukaka shi ne mafi sani.