Budewar kafar mace a ya yin yin sallah.
Tambaya
Mene ne hukuncin budewar kafar mace a lokacin da take sallah?
Amsa
Abin da aka tabbatar a shari’a shine, ya wajaba ga mace ta suturta dakkan jikinta in banda fuskarta da tafukan hannayenta, kamar dai yanda mafi yawan malamai suka tafi akai, amma wasu cikin malamai sun tafi akan cewa bai wajaba ma ga mace ta suturta kafafunta ba, shin a cikin sallah ne ko a wajen sallah.