Killace kayan masarufi domin neman samun kazamar riba.
Tambaya
Mene ne hukuncin killace kayan sayarwa da kuma yiwa masu saye badda-kama wurin kara farashi, domin samun kazamar riba?
Amsa
yan kasuwan da suke boye kayan sayarwa, ko suke boyewa domin sayarwa a farashi mai tsada domin amfana da karin da suka yi wurin samun kazamar riba, to sun aikata sabo, kuma za su samu zunubi, kuma ya kamata masu saye kar su goya musu baya wurin saye, don haka mai bukatar abu kar ya saya sai fa abinda yake tsananin bukatarsa.