Yin wasici ga daya daga cikin magada da yake da bukata ta musamman (Nakasassu).
Tambaya
Mene ne hukuncin yin wasici ga daya daga cikin magada da yake da bukata ta musamman (nakasassu)?
Amsa
Shari’a ba ta hana mutum ya yi wasici da wani kaso na gadonsa ga masu bukata ta musamman cikin magadansa ba, hasali ma sai sami lada ne akan wannan wasicin; saboda da haka ya wadatar da su ga barin tambaya da rokon mutane kenan.