Alamun manhajin Al Azhar
Tambaya
Mene ne alamun manhajin Al azhar? Shin kuma ya taƙaita ne da cibiyar addinin Musulunci ta Al Azhar kawai?
Amsa
Manhajin Al Azhar shi ne manhajin Ahlus Sunna wal jama’a a tsawon tarihi, ganin cewa cibiyar addinin Musulunci ta Al Azhar tana cikin daɗaɗɗun katangogin Ahlus Sunna na ilimi, da kuma irin babban rawar da ta taka a tarihi, da kuma irin babban matsayi na jagoranci da take yi ne ya sanya aka danganta mata wannan manhajin, shi alamun wannan manhajin sun haɗa manyan gunshiƙai guda uku; na farko: Imani da abin da Ahlus Sunna suka yi imani da shi, wato mazhabar Asha’ira da Maturidiyya da Fudhala’ul Hanabila, na biyu: Bin mazhabobin Fiƙihun Ahlus Sunna guda huɗu waɗanda aka bi su a zamanin magabata na ƙwarai, waɗannan mazhabobi sun haɗa da: Mazhabar Hanafiyya, da Malikiyya, da Shafi’iyya, da Hanbaliyya, na uku: Sufanci, a matsayinsa na hanyar tarbiyyar zukata da tsarin rayuwa zuwa ga Allah, duk wata cibiya, ko hukuma ta ilimi da take bin wannan manhajin wajen karantarwa da bayar da ilimi da kira zuwa ga Allah Maɗaukakin Sarki, to kuwa lallai tana kan manhajin Al Azhar na Ahlus Sunna mai daraja.