Iddar mai cikin da mijinta ya rasu
Tambaya
Mene ne iddar mace mai juna biyun da mijinta ya rasu ya bar ta da ciki?
Amsa
Iddar mai juna biyu yana karewa da zarar ta haihu; sawa’un rabuwar ta saki, ne ko kuwa ta rasuwa, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Su kuwa masu ciki lokacin iddarsu shi ne su haife abin da yake cikin cikinsu) [al- Talaq: 4], wannan aya ta hade har da wadda mijinta ya rasu ya barta da wasu ma.
Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.