Inshoran motoci
Tambaya
Shin ya halatta a yi inshoran motocin haya, ta yanda idan an yi hatsarin hanya, ko gobara ta tashi, ko an sace motar zai sa a biya kudin motar?
Amsa
Halal ne a yi inshoran motoci, domin yana cikin babin taimako da bayar da tallafi; hakikaninsa ma tallafi ne da gudummuwa ba wai ba ni in ba ka ba, yana kuma cikin taimakekeniya akan biyayya da tsoron Allah da aka bayar da umurnin a yi su a cikin maganar Allah Madaukakin Sarki da yake cewa: (Ku yi taimakekeniya akan biyayya da tsoron Allah) [al- Ma’ida: 2].
Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.