Kididdige daya bisa ukun dare da rabinsa
Tambaya
Ta yaya ake iya kididdige daya bisa ukun dare da rabinsa?
Amsa
Kididdige lokacin shiga dare yana farawa ne daga fadawar rana zuwa fitowan alfijir, to abin da ke tsakanin wadannan lokutan shi ne dare, domin sanin rabin wannan lokacin za a kirga awowin dake tsakani ne, inda za a raba gida biyu, sannan sai a kara kimar rabin lokacin zuwa lokacin magariba, sai a fitar da sauran rabin lokacin na rabin dare, ko a kasa lokacin gida uku sannan a sanya kimar lokacin daya bisa ukun lokacin zuwa lokacin magariba daga nan sai a fitar da daya bisa ukun daren.